Daga Aminu Bala Madobi
Mataimakin shugaban jam’iyyar APC na kasa shiyyar Arewa Sanata Abubakar Kyari, ya karbi ragamar shugabancin jam’iyyar ta kasa bayan tabbatar da murabus din shugaban jam’iyyar Abdullahi Adamu.
Alfijir Labarai ta rawaito Karbar ragamar ya biyo bayan murabus din da shugaban jam’iyyar na kasa Sanata Abdullahi Adamu ya yi a karshen mako.
Mista Adamu wanda ya kasance tsohon gwamnan jihar Nasarawa a karo na biyu ya mika takardar murabus din sa ga sakataren na kasa, Sanata Iyiola Omisore.
Da misalin karfe 10:40 na safiyar ranar Litinin ne mataimakin shugaban jam’iyyar na kasa ya jagoranci tawagar wasu ‘yayan jamiyyar guda bakwai zuwa wani taro a ofishinsa da ke hedikwatar jam’iyyar da ke Abuja.
An kuma rawaito cewa motar mataimakin shugaban kasa, an hango ya ajiye ta a saitin gurin da aka kebe wa shugaban kasa.
Mista Kyari tare da Mataimakin Shugaban Jam’iyyar na Kasa shiyyar Kudu Emma Enukwu; Mataimakin Shugaban (Arewa maso Yamma) Salihu Lukman; Mataimakin Shugaban (Arewa Maso Gabas) Salihu Mustapha; Mataimakin Shugaban (Arewa Ta Tsakiya) Muazu Bawa; Mataimakin shugaban (South West) Issacs Kekemeke; Mataimakin shugaban (kudu maso gabas) Ejoroma Arodiogu da mataimakin sakataren kasa Barista Festus Fuanter.
An tsaurara matakan tsaro a kusa da sakatariyar ta kasa tare da masu tuka mota zuwa titin Blantrye, inda hedkwatar jam’iyyar take, yayin da masu wucewa kuma ake dakatar da su domin amsa tambayoyi.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijir Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb