Tsohuwar ministar jin ƙai, Sadiya Umar Farouq ta bayar da uzurin rashin lafiya a matsayin dalilin da ya hana ta amsa gayyatar Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (EFCC).
Alfijir labarai ta rawaito bayanai sun ce tsohuwar ministar, ta nemi EFCC ƙara mata lokaci kan gayyatar titsiye da za a yi mata bisa zargin ta da hannu a badaƙalar halasta kuɗin haram har naira biliyan 37.1.
Hukumar EFCC dai na zargin tsohuwar ministar da almundahanar kuɗin da suka haura naira biliyan 37 tare da wani dan kwangila, James Okwete.
Sai dai kakakin hukumar ta EFCC, Dele Oyewale ya shaida wa Jaridar The Punch cewa, tsohuwar ministar ta aiko musu da lauyanta a matsayin wakili tare da neman karin lokaci domin amsa wannan gayyata, tana mai ba da uzuri na rashin lafiya da take damunta a yanzu.
Jami’an hukumar ta EFCC a jiya Laraba sun yi ta dakon tsohuwar ministar ta zamanin Shugaba Muhammadu Buhari a ofishinsu da ke Abuja, amma suka shafe sa’o’i ba tare da ganin keyarta ba.
A farkon makon jiya ne, Sadiya Umar Farouq ta fitar da wata sanarwa, wadda a ciki ta musanta hannu a badaƙalar da ake zargi.
Ta kuma yi iƙirarin cewa kwata-kwata ma ba ta san ɗan kwangilar da rahotanni ke cewa hukumar EFCC ta kama a binciken da take yi dangane da batun ba.
A makon jiya ne hukumar ta aika wa tsohuwar ministar goron gayyata sakamakon wani bincike da ta ƙaddamar a kan aikace-aikacen ma’aikatarta lokacin da take riƙe da muƙamin tsawon shekara shida.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/IUuk7jeH4yvAkwOmbOCSfl