Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Kano ta hana gwamnatin jihar Kano rusa ko sokewa ko kuma keta ginin gidan Alhaji Saminu Shehu Muhammad da ke no. 41 and 43 Salanta kan titin BUK.
Alfijir Labarai ta ruwaito cewa, a kwanan baya ne gwamnatin jihar Kano ta sanya wasu gine-gine a unguwar Salanta domin rugujewa, inda aka lalata katangar mafi yawan gidajen.
A ranar Juma’a ne babbar kotun tarayya ta bayar da umarnin dakatar da wasu mutane 12 da ake kara a karar da Alhaji Saminu Shehu Muhammad ya shigar.
Wadanda ake kara a cikin karar mai lamba: FHC/KN/CS/160/2023 sune Atoni-Janar na Jihar Kano, Lauyan Janar na Jihar Kano, Gwamnatin Jihar Kano, Ofishin Kula da Filaye na Jihar Kano, Hukumar Tsare-Tsare da Rarraba Birane ta Jihar Kano (KNUPDA).
Rundunar ƴan sandan Najeriya, Sufeto Janar na ƴan sanda, Kwamishinan ƴan sanda, Jihar Kano, Jami’an Tsaron Najeriya da Civil Defence na Jihar Kano.
Alkalin kotun, Mai shari’a S.A. Amobeda ya bayar da umarnin cewa duk wadanda ake kara da wakilansu da su dakatar da rusau har sai an yanke hukuncin da kotun ta yanke, bayan sauraron bukatar da mai kara ya shigar a gabatar.
Lauyan ya ba da umarnin a hanzarta sauraren karar, mai shari’a kuma ya dage sauraron karar zuwa ranar 10 ga Yuli, 2023.


Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijir Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/GdLiqZyHuSz5NhjdGoGRGZ