Alfijir Labarai ta rawaito gwamnatin jihar Legas ta fara shirin kawar da wasu gine-ginen da ke cikin mawuyacin hali a kasuwar Alaba da ke karamar hukumar Ojo ta jihar.
Tawagar jami’an tsaro na hukumar kula da gine-gine ta jihar Legas (LASBCA) sun fara atisayen hadin gwiwa a ranar Juma’a, 16 ga watan Yuni, 2023.
Tawagar da ta zagaya domin sake rufe wasu gine-gine da aka yiwa lakabi da mabambanta a baya.
LASBCA, ta ce matakin shine don hana bala’i.
Sun shawarci mazauna garin kan bukatar ficewa daga cikin gine-ginen da suka lalace wanda suka ce ya zama mai hadari ga mazauna.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/GdLiqZyHuSz5NhjdGoGRGZ
