Rundunar Yan Sandan Najeriya Ta Cafke Wani Shugaban Karamar Hukuma Bisa Zagin Bada Kwangilar Kisan Kai

FB IMG 1705963705564

Rundunar ‘yan sandan Najeriya tayi nasarar cafke wasu mutane biyu da ake zargi da hannu a wani yunkurin kisan gilla.

Alfijir labarai ta rawaito wadanda ake zargin sun hada da Shugaban daya daga cikin kananan hukumomin jihar Binuwai.

Binciken farko da aka gudanar ya nuna cewa shugaban karamar hukumar ya ba da kwangilar wasu ‘yan bindiga da niyyar kawar da kakakin majalisar dokokin jihar Benue, Hon. Aondona Hycenth Dajoh.

Jami’an Sashen Leken Asiri na Force – Intelligence Response Team (FID-IRT) sun yi gaggawar daukar mataki bayan samun sahihan bayanan sirri game da shirin kisan gilla.

A halin yanzu dukkan wadanda ake zargin suna hannun ‘yan sanda kuma suna bayar da hadin kai ga masu bincike kan binciken da ake yi.

Rundunar ‘yan sandan Najeriya na ci gaba da jajircewa wajen tabbatar da tsaro da tsaron ‘yan kasa da jami’an gwamnati.

Wadanda ake zargin za su fuskanci cikakken nauyin doka, kuma rundunar ‘yan sandan Najeriya ta kara tabbatar wa da jama’a a kan jajircewarta na tabbatar da doka da oda, da kuma rigakafin aikata laifuka a kowane mataki.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H3iC9eVfJI012LJzvCQn5V

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *