Rundunar Sojin Najeriya: ta tabbatar da Kashe Babban Abokin Bello Turji

FB IMG 1747612405146

A wani ci gaba da kokarin karya lagon ayyukan ta’addanci a yankin Arewa maso Yamma, Rundunar Jiragen Sama ta Operation Fasan Yama ta kai mummunan hari a ranar 18 ga Mayu, 2025, wanda ya yi sanadiyyar kashe Alhaji Shaudo Alku, daya daga cikin manyan abokan Bello Turji.

Shaido daga cikin rahotannin leken asiri sun tabbatar da cewa an kai harin ne a kusa da Makarantar Firamare ta Tunfa, da ke karamar hukumar Isa, Jihar Sokoto. Alku, wanda aka gayyata daga Jamhuriyar Nijar domin wani taro na sirri, ya mutu tare da wasu daga cikin mabiyansa da kuma wasu kwamandoji da ake zargin suna cikin jerin shugabannin ‘yan ta’adda.

Wannan hari ya janyo ce-ce-ku-ce a tsakanin jama’a, inda da dama ke yabawa rundunar sojin sama bisa wannan nasara mai muhimmanci. Wannan mataki yana daga cikin jerin hare-haren da ake kaiwa don rushe sansanonin ‘yan ta’adda da kuma tabbatar da tsaron al’umma.

Hedikwatar Sojin Najeriya ta bayyana cewa za a ci gaba da kai irin wadannan hare-haren har sai an tabbatar da cewa yankin ya tsira daga ayyukan ta’adanci.

Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news ku shiga nan  👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/KoLt2IMlnQfJPP6zNrcNKD

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *