Rundunar sojan Nijeriya ta kama fiye da sojoji da ‘yan sanda 20 bisa zargin sayarwa ‘yan ta’adda makamai

IMG 172251 30525 1748622318488

Rundunar sojan Nijeriya ta kama fiye da sojoji da ‘yan sanda 20 saboda zargin sayar wa da ‘yan ta’adda makamai da aka sace daga sojojin kasar, kamar yadda wani jami’in soja ya bayyana.

Kakakin Rundunar Sojojin da ke yaƙi da ‘yan ta’adda mai hedkwata a jihar Borno Kyaftin Reuben Kovangiya, ya ce kamen wani bangare ne na yaƙi da cinikin makamai da harsasai.

Kafofin watsa labarai na cikin gida sun ruwaito cewa an kama sojoji 18, da ‘yan sanda 15 da fararen hula takwas.

“Wannan wani ɓangare ne na aikin yaki da cinikin makamai da harsasai da ake gudanarwa a dukkanin wuraren aiki,” kamar yadda Kovangiya ya bayyana wa kamfanin dillancin labarai na Reuters. “Idan wani ma’aikaci ya aikata wani abu da zai cutar da tsarin, za a kama shi kuma a gurfanar da shi a gaban kuliya.
Kovangiya bai yi karin bayani kan nau’i da adadin makaman da aka sayar ba, amma ya ce za a gurfanar da waɗanda ake zargin a gaban kotu.

A bana, Najeriya ta fuskanci ƙaruwar hare-hare daga ‘yan ta’addan ƙungiyar Boko Haram da reshenta, Daesh, waɗanda suka ƙwace wasu sansanonin sojoji a jihar Borno da ke arewa maso gabas. A mafi yawan hare-haren, sun kwace makamai daga sansanonin sojoji.

For more information about Alfijir labarai/Alfijir news follow here 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Advart Number+2348032077835

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/KoLt2IMlnQfJPP6zNrcNKD

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *