Tsohon gwamnan jihar Sokoto, kuma mamba a kwamitin amintattu na jam’iyyar PDP, Alhaji Attahiru Bafarawa, a ranar Lahadi, ya nuna damuwarsa kan ayyukan ƴan bindiga a yankin Arewa maso-Yamma da kuma Arewa maso-Gabas, inda ya bayyana fargabar cewa hakan ka iya haifar da matsalar karancin abinci.
Alfijir Labarai ta rawaito Bafarawa ya ce, ya kamata gwamnatin shugaba Bola Tinubu ta dauki batun samar da abinci a matsayin daya daga cikin abubuwan da ta saka a gaba.
Ya kuma yi gargadin cewar, idan ba a dauki tsauraran matakai na dakile tashe-tashen hankula ba, Arewa za ta fuskanci koma bayan ilimi mai tsanani.
Bafarawa ya ce, “Maimakon maganar naɗin ministoci, tallafin mai da kuma tattalin arziki, kamata ya yi gwamnati ta yi la’akari da batun samar da abinci domin a halin da muke ciki, nan da watanni uku masu zuwa, tabbas za mu fuskanci matsaloli a Najeriya, musamman a Arewa maso-Yamma.
“’Ƴan bindiga sun ki barin manoma su yi noma. Wannan lamari dai ya na da matukar hadari, ba wai kawai yan bindigar na kashe mutane ba, har ma da karancin abinci zai yi tsanani nan da wasu watanni masu zuwa, musamman a yankin Arewa maso Yamma da Arewa maso Gabas. Don haka mu na son gwamnati ta farka ta yi wani abu a kai,” in ji shi.
The Punch
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijir Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/GdLiqZyHuSz5NhjdGoGRGZ
Hakika maganar sa abinda yakamata a duba ne kuma da gaggawa musamman ga ita Gwamnatin tarayya.
Tabbas idan ba Noma ba maganar Abinci.