Rashin Iya Mulki Ya Janyo Rashin Tsaro A Arewa Maso Yammacin Najeriya – Kashim

Yana da matukar muhimmanci ga arewa ta fara shirin sake fasalin yankin da kuma sake farfado da shi don sake mayar da shi domin a samu ci gaba cikin sauri

Alfijir Labarai ta rawaito Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ya ce rashin shugabanci na da alhaki kai tsaye kan yawaitar ‘yan fashi da garkuwa da mutane a shiyyar arewa maso yamma.

Shettima ya yi wannan jawabi ne a lokacin da ya karbi bakuncin kungiyar hadin kan ‘yan kasuwa, masana’antu, ma’adanai, da noma na jihohin Arewa, CONSCCIMA, a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Mataimakin shugaban kasar ya ce daidaita yanayin mulki a al’amuran arewa ya zama dole, domin a maida yankin zuwa ci gaba.

Arewa maso yamma ta ƙunshi jihohi bakwai Jigawa, Kaduna, Kano, Katsina, Kebbi, Sokoto, da Zamfara.

Musamman jihohin Zamfara, Katsina da Sokoto sun kasance wuraren da ‘yan fashin daji suka addabi jama’a, lamarin da ya janyo sace mutane da kashe-kashe a ‘yan kwanakin nan.

Shettima ya ce masu ruwa da tsaki a yankin arewa baki daya dole ne su sake duba yadda al’amuran yankin suke, sannan su fito da kwararan matakai na sake farfado da al’ummarmu.

Yana da matukar muhimmanci ga arewa ta fara shirin sake fasalin yankin da kuma sake farfado da shi don sake mayar da shi domin a samu ci gaba cikin sauri in ji Shettima.

Yawancin batutuwan da shugaban CONSCCIMA ya bayyana suna da matukar tayar da hankali, domin wadannan batutuwa ne da suka shafi rayuwa da jin dadin jama’armu.

Ba za a taba samun ci gaba ba tare da zaman lafiya ba, kuma ba za a taba samun zaman lafiya ba tare da ci gaba ba

Musamman a arewa maso yamma ta hanyar shirin Pulaku.

Shirin na Pulaku shine mafita da zai magance ƙalubalen da ke addabar yankin arewa maso yamma.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Alfijir Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/Jmw5CBsPV6H3DbSgnlFUHM

One Reply to “Rashin Iya Mulki Ya Janyo Rashin Tsaro A Arewa Maso Yammacin Najeriya – Kashim”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *