PSC ta kafa kwamitin ɗaukar sabbin ƴan sanda a Najeriya

Shugaban hukumar kula da aikin ɗansanda, PSC, Dr Solomon Arese, a jiya Litinin a Abuja ya kaddamar da kwamitin mutum 11 domin daukar gudanar da aikin ɗaukar aikin ma’aikata ɗasanda.

Alfijir Labarai ta rawaito Kwamitin zai tantance tare da bayyana guraben aiki a rundunar ‘yansandan Najeriya (NPF) da ake da bukatar cikewa tare da tsara ka’idojin kowane tsarin daukar ma’aikata a rundunar.

“Za kuma su tantance tsarin da za a yi amfani da su ta yanar gizo wajen tallata ɗaukar aikin da sanya tallace-tallace a jaridun kasar nan da sauran hanyoyin yada bayanai kan daukar ma’aikatan.

“Haka zalika zai tabbatar da daukar ma’aikatan da suka cancanta, ’yan Najeriya masu kwarewa a cikin rundunar ‘yan sandan Najeriya ba tare da nuna bambancin jinsi, addini, ko ɓangaranci ba,” in ji shi.

Mista Arese ya ce kaddamar da kwamitin wani muhimmin ci gaba ne ba ga PSC da rundunar ‘yansandan Najeriya kadai ba, har ma da sauran hukumomin tsaro na Nijeriya.

Ya ce kaddamar da kwamitin ya yi daidai da daya daga cikin hurumin hukumar, kamar yadda ya tabbatar da kuma karfafawa a hukuncin da kotun koli ta yanke a ranar 11 ga watan Yuli.

Ƴan kwamitin sun hada da Cif Onyemuche Nnamani, mai wakiltar PSC a matsayin shugaba; Bala Ciroma, daga rundunar Yan sandan Najeriya; da Muhammed Magaji, daga ma’aikatar harkokin ‘yan sanda.

Sauran sun hada da Dr Ifeoma Anyanwutaku, PSC; Farfesa Joseph Olowofela, Hukumar kula da Ƙa’idojin ɗaukar aiki ta Tarayya; Hassan Yabanet, Kwalejojin ‘yan sanda; da Yusuf Sanusi, PSC.

Sauran mambobin hukumar sun hada da Sani Hada, Victoria Onyekwuluije da Ahanmisi Obehi, dukkansu daga PSC, yayin da Olabode Akinbamilowo na rundunar ‘yan sandan Najeriya zai zama Sakatare.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@musa_bestseller

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai  👇

https://chat.whatsapp.com/Jmw5CBsPV6H3DbSgnlFUHM

4 Replies to “PSC ta kafa kwamitin ɗaukar sabbin ƴan sanda a Najeriya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *