Pakistan ta yi alƙawarin ba Iran cikakken goyon baya a yaƙin da take da Isra’ila

IMG 134726 14625 1749905266792

Pakistan ɗin ta buƙaci ƙasashen Musulmi su haɗe wa Isra’ila kai inda ta ce idan ba su haɗa kansu yanzu ba, dukkansu matsalar za ta shafe su.

Ƙasar Pakistan ta yi alƙawarin “goyon bayan Iran” tare da kiran Musulman duniya su haɗe wa Isra’ila kai bayan ta ƙaddamar da hari kan Iran.

Ministan Tsaron Pakistan Khawaja Asif ne ya bayyana haka a Majalisar Dokokin Pakistan inda ya buƙaci ƙasashen Musulmi su fito da wani tsari ta yadda za su haɗe wa Isra’ila kai.

“Isra’ila ta kai hari kan Iran da Yemen da Falasɗinu. Idan Musulmi ba su haɗa kansu yanzu ba, dukkansu matsalar za ta shafe su,” in ji shi.

Ya buƙaci kasashen musulmi da ke da alakar diflomasiyya da Isra’ila su gaggauta yanke huldar su, ya kuma ce kamata ya yi kungiyar hadin kan kasashen musulmi OIC ta yi taro domin tsara dabarun haɗin gwiwa.

Asif ya ce Pakistan na da alaka mai ƙarfi da Iran kuma Islamabad tana goyon bayan Tehran a wannan mawuyacin lokaci.

“Muna goyon bayan Iran kuma za mu tallafa musu a kowane taron kasa da kasa domin kare muradunsu,” in ji ministan tsaron kasar.

TRT

Ga Masu Son Bada Talla A Kira   +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news ku shiga nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/KoLt2IMlnQfJPP6zN

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *