Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA) ta ce jihohi 14, za su iya fuskantar ruwan sama kamar da bakin kwarya wanda zai iya haifar da ambaliya daga ranar 4 zuwa 8 ga watan Yuli a duk faɗin ƙasar.
Alfijir Labarai ta rawaito hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Mista Ibrahim Farinloye, Kodinetan yankin, NEMA, ofishin yankin Legas ya sawa hannu.
Farinloye ya bukaci masu ruwa da tsaki a jihohin da abin ya shafa da su dauki matakan kariya domin dakile asarar rayuka da dukiyoyi.
Ya lissafa jihohi da al’ummomi a matsayin Plateau: Langtang da Shendam;
Jihar Kano: Sumaila, Tudun wada;
Jihar Sokoto: Shagari, Goronyo da Silame;
Delta: Okwa.
Sauran sun hada da jihar Kaduna: Kachia;
Akwa Ibom: Upenekang;
Adamawa: Mubi, Demsa, Song, Mayo-Belwa, Jimeta, da Yola;
Jihar Katsina: Katsina, Jibia, Kaita da Bindawa.
Ya kuma kara da jihar Kebbi: Wara, Yelwa da Gwandu;
Zamfara: Shinkafi da Gummi
Borno: Briyel;
Jigawa: Gwaram;
Kwara: Jebba;
Nijar: Mashegu da Kontagora
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijir Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/GdLiqZyHuSz5NhjdGoGRGZ
