Alfijr ta rawaito Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA ta kwace fiye da kwayoyi miliyan 100 na opioids da Tramadol a cikin watanni 22.
Babban jami’in gudanarwa na hukumar, Brig. Janar Mohammed Marwa ne ya bayyana a ranar Talata, ya ce haramtattun kayayyaki na iya yin illa ga matasa a fadin ƙasar.
Da yake jawabi a wajen bikin bayar da lambar yabo ta Commands/Commendation da kuma ado na sabbin jami’an da aka samu karin girma a hedikwatar Hukumar, Abuja, ya ce; “A cikin wa’adin da hukumar ta dauka, ta kama masu safarar miyagun kwayoyi guda 23,907 ciki har da Madugun dillacin kwaya guda 29.
Hakazalika an kama fiye da tan 5,500 ko kuma kilogiram miliyan 5.5 na haramtattun kwayoyi, wadanda kudadensu sun kai sama da Naira biliyan 450.
Ya sake cewa, mun wani sumame kan masu noman wiwi ta hanyar lalata gonakin wiwi 772. 5.
A cikin wadannan watanni 22, mun samu nasara kamawa da daure mutane 3,434 masu laifi a Kurkuku.
A wani bangare na yunkurin rage tu’ammali da miyagun magunguna adadin waɗanda aka ba da shawara, da gyara hali ya kai 16,114.
Ya Kara da cewar, a dauki misali, kwayar tramadol miliyan dari da aka kama a cikin watanni 22 da suka gabata Idan da a ce wadannan kwayoyin an bari sun yadu cikin matasa, zai yi matukar illa ga rayuwar su.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇