Daga Aminu Bala Madobi
Tsohon mai baiwa mataimakin shugaban kasa shawara kan harkokin siyasa, Dakta Hakeem Baba-Ahmed, ya yi gargadin cewa Najeriya za ta iya wargaje idan har gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu ta yi magudi a zaben 2027.
Da yake magana a wata hira ta faifan bidiyo a Kaduna, Baba-Ahmed, wanda ya bayyana tare da Farfesa Usman Yusuf, tsohon babban sakataren hukumar inshorar lafiya ta kasa (NHIS), ya kuma bayyana cewa babu wani dan siyasa da zai iya lashe shugabancin Najeriya a 2027 ba tare da goyon bayan yankin Arewa ba.
Ya kuma yi gargadin cewa an mayar da Arewa saniyar ware, yana mai cewa ci gaba da wofintar da yankin zai haifar da sakamakon da ba a zata ba.
Tabbas Najeriya na kan hanyar rugujewa idan Tinubu ya murde zaben kakar 2027.
Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news ku shiga nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/KoLt2IMlnQfJPP6zNrcNKD