
Alfijr ta rawaito Gwamnan Ganduje ya yi kira ga al’ummar jihar Kano da su yafe masa.
Yayi wannan kiarn ne Yayin da ya halarci tafsirin Alkur’ani mai girma a masallacin Al-Furqan da ke birnin Kano.
Ganduje ya ce dole ya nemi afuwar Kanawa, kasancewar ‘yan kwanaki ne kawai suka rage masa ya sauka daga mulkin jihar
Ya ƙara da cewa ya yafe wa duk wanda ya ɓata masa ko yayi wata magana akansa, sannan shi ma yana neman duk wanda ya ɓatawa da su yafe masa.
”Wa’adina na mulkin jihar Kano ya zo ƙarshe, ina yi muku bankwana, kuma ina yi muku fatan alkairi, kuma waɗanda muka ɓata wa, dama babban malami ya faɗi muhimmancin yafiya”, in ji Ganduje.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu aFacebook. Alfijr Labarai YouTube. Best Seller ChannelTwitter. @MusabestsellerInstagram. @musa_bestsellerKo a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇https://chat.whatsapp.com/G1wNveF9mGU7jec5mWhFvZ
Allah ya yafe mana, Amma ka danne mana haqqoqi da yawa