Tsohon shugaban ƙasar Najeriya na mulkin soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida, ya bayyana cewar tuni ya hango wanda zai gaji buzun kujerar shugaba Buhari a kakar zaɓe ta 2023.
Jaridar Daily Independent Hausa 24 ta rawaito Ibrahim Badamasi Babangida IBB ya bayyana haka ne a wata tattaunawa da akayi da shi a gidan TV (Arise TV)
“IBB yace Naga wani matashi da shekarunsa basu wuce 60 ba ya ɗare kujerar shugaban ƙasar Najeriya a 2023.”
kuma wannan matashi ya haɗa duk wata cancanta da nagarta da Najeriya ke buƙata idan har aka bashi damar tsayawa.
IBB ya sake cewa ” Ina shawartar ƴan Najeriya da kada su sake su zaɓi mutumin da ya haura shekaru 60 a matsayin shugaban ƙasa.”
“Halin da Najeriya take ciki a yanzu tana buƙatar jagorancin matashi mai ƙwarewa a fannin tattalin arziki da iya siyasa, wanda yake da abokai a dukkan sassan ƙasar nan, wanda ya iya tafiyar da al’umma.” kamar yadda Labarai 24 ta wallafa, a Cewar IBB
Wa kuka Hango a ranku?
A hasashen da IBB yayi?
Kwankwaso ne