Mutum 3 Sun Mutu Wasu Sun Jikkata A Hatsarin Mota A Kano


Alfijr ta rawaito Kakakin Hukumar Kashe Gobara ta Jihar, Saminu Yusuf Abdullahi, ne ya sanar da faruwar lamarin, cewa hatsarin ya auku ne a kan gadar sama da ke kan hanyar zuwa gidan Gwamnatin jihar, a ranar Talata.

Ya kara da cewar, hatsarin ya faru ne da wata mota kirar leta-hayis wacce ta taso daga garin Ajingi ta shiga cikin garin Kano, inda a nan ne murfinta ya daki wani bangaren gadar saman.

Wannan dalilin ya sa motar ta kama da wuta bayan murfin ya fice daga jikinta..

Saminu ya ƙara da cewa, bayan aukuwar hatsarin, jami’ansu sun je wurin inda suka kwashe gawarwaki tare mutanen da suka jikkata zuwa Asibitin Kwararru na Murtala Muhammad da ke Kano, inda aka tabbatar da rasuwar mutum uku.

Ya ce yanzu haka ragowar wadanda suka jikkata suna can a asibitin suna samun kulawar gaggawa.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook.   Alfijr Labarai
YouTube.     Best Seller Channel
Twitter.        @Musabestseller
Instagram.  @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/G1wNveF9mGU7jec5mWhFvZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *