Alfijr ta rawaito wasu gungun ƴan daba sun kai hari kan ayarin yakin neman zaben dan takarar Sanatan Kano ta Tsakiya na Jam’iyyar APC, Abdulsalam Abdulkarim Zaura.
Daraktan yakin zaben A.A Zaura, Yahaya Adamu, ya ce lamarin ya faru ne a ranar Asabar a yankin Gayawa a Karamar Hukumar Ungogo a Jihar Kano.
Takardar da ya aike wa kwamishinan ’yan sandan jihar da ’yan jarida ta ce, “Bincikenmu ya gano zuwa yanzu mutum 17 ne suka samu rauni sakamakon harin da aka kai mana.
“Wadanda suka ji rauni suna Asibitin Murtala ana kula da su, sannan motocinmu 17 duk an lalata su.”
Adamu ya bukaci kwamishinan ’yan sandan jihar ya gudanar da bincike tare da daukar matakin da ya dace.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇