Mutane 25 Ne Suka Mutu, 10 Suka Jikkata A Wani Mummunan Hatsarin Da Ya Afku A Bauchi

Alfijr ta rawaito a kalla mutane 25 ne suka rasa rayukansu a wani hatsarin da ya afku a hanyar Hadeja zuwa Potiskum a karamar hukumar Gamawa a jihar Bauchi.

Wasu 10 sun samu raunuka daban-daban a hatsarin daya tilo da ya hada da wata motar bas Toyota Hummer.

Hadarin ya afku ne a ranar Alhamis da karfe 4:30 na yamma.

Kwamandan hukumar kiyaye hadurra ta tarayya reshen jihar Bauchi Yusuf Abdullahi ne ya tabbatar wa da wakilinmu afkuwar lamarin a safiyar Juma’a.

Ya ce jimillar mutane 35 da suka kunshi manya maza 19, manya mata 11, yara maza biyu da mata uku.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/G1wNveF9mGU7jec5mWhFvZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *