Mutane 15 Sun Mutu, 7 Sun Jikkata A Wani Hatsarin Mota Da Ya Afku A Bauchi

Alfijr ta rawaito wani Mummunan Hadari ya rutsa da wasu mutane a karamar hukumar Toro ta jihar Bauchi, inda mutane 15 suka mutu a wani hatsarin mota da ya afku a kauyen Nabordo.

Mista Yusuf Abdullahi, babban kwamandan hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC), ya bayyana cewa hatsarin ya hada da mota kirar guda daya da wata motar bas Toyota Hiace.

Ya kuma bayyana cewa wasu mutane bakwai sun samu munanan raunuka a hadarin wanda ya faru da misalin karfe 3:30 na rana.

Abdullahi ya dora alhakin faduwar hatsarin a kan rashin iya sarrafa su, da keta gudu da kuma tukin ganganci.

“Mutane 22 ne hatsarin ya rutsa da su a hanyar, akwai manya maza 18, manya mata biyu, mace daya da namiji daya.

“Sha biyar daga cikin mutanen, manya maza 12, babba mace daya da yaran biyu sun rasa rayukansu a nan take.

“Wasu bakwai, manya maza shida da mace daya sun sami raunuka daban-daban,” in ji shi.

Ya kara da cewa an kai wadanda suka jikkata zuwa Asibitin Koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi domin yi musu magani, yayin da aka ajiye gawarwakin a dakin ajiye gawa na asibitin.

Yayi kira ga masu ababen hawa da su tabbatar da cewa suna da tayoyi masu kyau, kula da ka’idar tuki, matsakaicin gudu, kula da abin hawa na yau da kullun da kuma kasancewa cikin nutsuwa yayin tuki.

       Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai

https://chat.whatsapp.com/KrigvNKcneVBHxctLUQ0ux

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *