Mun Dakatar Da Zanga-Zanga Bayan Da Tinubu Ya Tabbatar Da Karin Albashi

NLC da TUC sun sanar da cewa za su tsagaita da zanga-zanga domin su ba gwamnati damar cika alkawuran da ta daukar wa ’yan Najeriya.

Alfijir Labarai ta rawaito Shugaban Kasa Bola Tinubu ya gayyaci shugaban NLC, Joe Ajaero da na TUC, Festus Osifo, domin tattaunawa a Fadarsa da yammacin Laraba.

Ajaero ya shaida wa ’yan jaridar Fadar Shugaban Kasa bayan kammala taron cewa, bayan tattaunawar, sun amince su ba gwamnatin karin lokaci domin ganin kamun ludayinta.

Ya kara da cewa babbar nasarar da zanga-zangarmu da ta samu ita ce bukatar Shugaban Kasa, na  tattaunawa da mu a sirrance.

Hakazalika mun tattauna muhimman bayanai kan abubuwan da suka taso bayan janye tallafin tare da wasu muhimman batutuwa.

Daga ciki ya tabbatar mana da cewa za a farfado da matatar man fetur ta Fatakwal, kuma za ta fara aiki nan da watan Disamba.

Ya kuma yi mana alkawarin cewa za a kara wa ma’aikata mafi karancin albashi nan ba da jimawa ba.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook.   Alfijir Labarai
YouTube.     Best Seller Channel
Twitter.        @Musabestseller
Instagram.  @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai  👇

https://chat.whatsapp.com/BW0j8s7exuQ7ojpyCVMtfI

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *