Matasa karku bari ayi amfani da ku wajen tada hankalin al’umma a yayin bukukuwan Sallah – Alh Musa Jidda Dan Adalan Mubi

IMG 152705 05625 1749133775433

Alh Musa Jidda Ɗan Adalan Muni Sarki yayi kira ga al’umma musamman matasa kan rungumar zaman lafiya yayin shagulgulan bikin Sallah ke zuwa da kuma ko wane lokaci.

Ɗan Adalan Mubi yayi wannan kiran ne a yayin wata tattaunawrsa da jaridar Alfijir labarai a Kano, inda ya bukaci matasa da daukacin al’ummar jihar da su tabbatar da zaman lafiya da fahimtar juna a wannan lokaci na bikin sallah

Ya kara da cewar babban abinda ya kamata aga matasa sun maida hankali akai shine neman ilimi da sana’a, domin idan ka zama mara ilmi da dogaro da kai tabbas rayuwa ta dauko hanyar lalacewa! Wanda ba shine fatanmu ba.

A karshe Alh Musa Jidda Ɗan Adalan Mubi Saraki yace “Muna taya daukacin Musulmin Duniya da na Najeriya da mazauna Kano murnar zagayowar wannan lokaci mai albarka. Allah ya maimaita mana Allah ya kara mana lafiya da zaman lafiya baki daya ameen.

Ga Masu Son Bada Talla A Kira   +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news ku shiga nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/KoLt2IMlnQfJPP6zN

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *