Idan har zamu tausayawa Rarara mu roka masa Allah ya bayyana mahifiyarsa saboda halin da ta tsinci kanta a ciki, banga dalilin da zaisa Rarara ya sakawa ƴan arewa da waƙar izgili ba, bayan fitowarta.
Wannan waƙar da mawaki Rarara yayi tamkar yaci albasa ne da yawun yan Arewa, adede lokacin da ƴan kasa ke cikin talauci da rashin tsaro..
Na rantse da Allah ko kokonto banayi Dauda Kahutu Rarara ba masoyin Yan Najeriya bane. In har Shugaban Najeriya zai fito ya bawa yan kasa haƙuri akan tsananin Rayuwa taya zaka fitar da sabuwar waka don sake fusata matasa da ƴan Najeriya da wakarka?
Wallahi mawaki Dauɗa Kahutu Rarara kaji tsoron Allah, ka sani akwai ranar kin dillancin ranar da kudi da dukiya ba zasu maka amfani ba sai wanda ya je gaban Allah da kyakyawar zuciya ta imani.. Inji Barrah Almadany..
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj