Mataimakin Gen Abacha, Oladipo Diya Ya Rasu

Alfijr ta rawaito Laftanar Janar Oladipo Diya, wanda ya yi mataimakin shugaban ƙasar Najeriya zamanin mulkin Janar Sani Abacha ya rasu.

Janar Oladipo Diya ya rasu ne a safiyar Lahadi a wani asibiti dake Legas, ya na da shekaru 78.

Babban ɗan marigayin, Oyesinmilola Diya ne ya sanar da rasuwar ta sa.

An dai haifi Oladipo Diya ne a garin Odogbolu dake jihar Ogun a ranar 3 ga Afrilu, 1944.

A zamanin mulkin soja na Janar Muhammadu Buhari ya zama gwaman jihar Ogun daga Janairun 1984 zuwa Agustan 1985.

Daga nan ya zama Babban Hafsan sojin Najeriya, inda daga bisani likkafa ta ci gaba ya zama mataimakin shugaban ƙasa Janar Sani Abacha.

Sai dai Janar Abacha ya tuhumi Janar Diya da yunƙurin yi masa juyin mulki.

Kuma kotun soji ta tabbatar masa da laifin har ta yanke masa hukuncin kisa.

Amma kafin zartar da hukuncin Allah ya yi wa Janar Abacha rasuwa.

Gwamnatin Janar Abdulsalami Abubakar kuma ta sake shi.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/G1wNveF9mGU7jec5mWhFvZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *