Majalisar jihar Kano zata saukewa ɗan Adaidaita sahun da ya tsinci Makudan kudade kabakin arziki


Shugaban majalisar dokokin jihar Kano Rt.Hon.Jibiril Isma’il Falgore yace majalisa zata gayyaci Auwal Salisu domin girmamashi tare da bashi gudun mawa daga cikin albashin kowanne Dan majalisa

Alfijir Labarai ta rawaito ya bayyana hakan lokacin da suke zaman majalisar a yau Litinin, ya kara da cewar za suyi hakan ne  domin ya bawa wanna yaro mai kananun shekaru, kuma yake da imanin mai da wadannan makudan kudade duk kuwa da cewa su talakawa ne.

Dan sahun Mai suna Auwal Salisu ya dauki mutane biyu ne, bayan ya sauke su yaga sun manta da wani buhu, nan take ya bude yaga kudi ne sai ya koma idan ya aje su amma bai same su ba.

Inda ya Kai kudin ga mahaifan shi suma suka goyi baya wajen aje kudin da jiran ta idan za a nemi kudin sai gashi mahaifiyar shi taji a gidan radio Arewa ana cigiyar kudin idan sukai gidan radio domin Maidawa Mai kudin kayan shi.

Dan majalisar da ya kawo kudirin na gaggawa Hon Salisu Muhammad Doguwa ya bukaci majalisar data nemi gwamanatin kano ta taimakawa yaro da iyayen shi, bisa irin wannan gaskiya da ya nuna a wannan lokacin da ake cikin na matsin rayuwa, kuma ta ayyana shi amatsayin gwarzon shekara ta 2023.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai  👇

https://chat.whatsapp.com/FNim39ly65N2CzcTt8FgWb

One Reply to “Majalisar jihar Kano zata saukewa ɗan Adaidaita sahun da ya tsinci Makudan kudade kabakin arziki”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *