Majalisar Dokokin Kogi Ta Dakatar Da Mambobi 9 Da Wasu Ciyamomi 5

Daga Aminu Bala Madobi

Alfijr ta rawaito cewa Majalisar dokokin jihar Kogi ta dakatar da mambobinta tara a yau alhamis.

Rahotanni sun ce an dakatar da su ne a wani zama da aka yi a yau Alhamis, 23 ga Maris, 2023.

Haka ma majalisar ta dakatar da shugabannin kananan hukumomi tara a jihar.

Hakan na zuwa ne kwanaki kadan bayan zabukan gwamnoni da na ‘yan majalisun jihohi a fadin kasar.

Jam’iyyar APC mai mulki ta lashe kujeru 22 daga cikin 25 na majalisar dokokin jihar Kogi yayin da jam’iyyar PDP ta samu kujeru biyu yayin da African Democratic Congress (ADC) ta samu guda daya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *