Alfijr ta rawaito majalisar dokokin jihar Kebbi ta gayyaci gwamnan jihar, Abubakar Atiku Bagudu kan amfani da bashin Nera Milyan Dubu 18.7 daga gwamnatin tarayya.
A cikin wasikar da majalisar ta aikewa gwamnan mai kwanan wata 26 ga watan Janairu, 2023 da solacebase ta gani, majalisar ta bukaci gwamnan ya bayyana a gabanta a ranar Juma’a 27 ga watan Janairu, 2023.
A cewar wasikar hakan ya yi daidai da kokarin da majalisar ta yi na tabbatar da kula da dukiyar jihar cikin tsanaki .
Wasikar ta kasance kamar haka: Dangane da bukatar ku na amincewa da Gwamnatin Kebbi ta karbo bashin kudi daga gwamnatin tarayya mai kwanan wata 18 ga Oktoba, 2021 tare da mai lamba No. GHBK/8/21 Vol.1
‘’ Majalisar Dokokin Jihar Kebbi ta amince da kudi har sama da Naira Miliyan Dubu Goma sha Takwas (18,746, 059,992.57) ta hanyar kudiri mai kwanan wata 18 ga Oktoba, 2021.’’
A ci gaba da kokarin da take yi na kula da albarkatun kasa cikin tsanaki majalisar tana neman Gwamnan da ya gurfana a gaban majalisar domin yin bayani kan yadda za ayi amfani da kudaden a ranar Juma’a 27 ga Janairu, 2023 da karfe 10:00 na safe.
Jaridar solacebase ta rawaito cewa wasikar da Suleiman Shamaki, mukaddashin magatakardar majalisar ya sanyawa hannu tana mai take ‘’Re: Offer of Federal Loan Facility’’.
An makala wasikar ne tare da sanya hannun ‘yan majalisa 20 daga cikin 24 na majalisar.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇