Majalisar Dattawan Najeriya Ta Tantance El-Rufai Da Sauran mutane 13


Majalisar dattawa ta fara tantance sauran mutane 14 da aka nada a matsayin ministoci kamar yadda shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bukata tun farko.

Alfijir Labarai ta rawaito Cikin wadanda aka tantance a yau akwai tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai da Sanata David Umahi, tsohon gwamnan Ebonyi wanda kuma shine mataimakin jagoran majalisar dattawa.

A ranar Alhamis 28 ga watan Yuli ne dai shugaba Tinubu ya mika jerin sunayen ministoci 28 zuwa ga zauren majalisar, inda ya bukaci ta tantance tare da amincewa da sunayen domin nada su a matsayin ministocin tarayyar Najeriya.

A saboda haka ne majalisar dattawa ta fara aikin a ranar Litinin, inda ta tantance 14 daga cikin su.

Wadanda ke cikin jerin sunayen sune:
David Umahi (Ebonyi) A

debayo Edun (Ogun)

Nasir El-rufai (Kaduna)

Ahmed Dangiwa (Katsina)

Uche Nnaji (Enugu)

Stella Okotete (Delta)

Dele Alake (Ekiti)

Adekola Adelabu (Oyo)

Muhammad Idris (Niger

Farfesa Ali Pate (Bauchi)

Doris Uzoka (Imo)

Lateef Fagbemi (Kwara)

Ekperikpe Ekpo (Akwa Ibom

Hannatu Musawa (Katsina)

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook.   Alfijir Labarai
YouTube.     Best Seller Channel
Twitter.        @Musabestseller
Instagram.  @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai  👇

https://chat.whatsapp.com/BW0j8s7exuQ7ojpyCVMtfI

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *