Majalisar Dattijan Najerya ta buƙaci gwamnatin ƙasar ta haɗa kai da Majalisar Dinkin Duniya domin yin kira a tsagaita wuta a hare-haren da Isra’ila ke kai wa zirin Gaza.
Alfijir Labarai ta rawaito a wani kudiri da Sanata Abdulrahman Kawu Sumaaila daga Kano ya tsara, aka kuma gabatar da shi jiya Talata a gaban majalisar bayan zazzafar muhawara, yanzu dai baki ya haɗu wajen neman Najeriya ta bayyana matsayarta a rikicin na Gaza.
Majalisar Dattawar ta bayyana mace-mace da kuma adadin waɗanda suka rasa muhallansu sakamakon rikicin na Isra’ila da Hamas a matsayin abin tsoro.
A tattaunawarsa da BBC Sanata Kawu Sumaila ya ce sun yi la’akari da abubuwan da suke faruwa sun kai maƙura da ya kamata Najeriya ta bayyana matsayarta kan wannan rikici.
“Kamar bai kamata ba idan aka yi la’akari da da matsayinmu a duniya da kuma Afrika a ce mun naɗe hannu mun yi shiru.
“Shi yasa muka haɗu muka zo da wannan kuɗuri ga ita gwamnatin Najeriya domin ta haɗa hannu da MDD wajen ganin an kawo ƙarshen wannan abu da ke faruwa,” in ji Kawu Sumaila.
Sanatan ya ce buƙatar Majalisar ta biyu ita ce ta nuna goyon bayan bai wa ko wanne ɓangare tsakanin (Isra’ila da Falasdinu) gashin kansa.
“Menene abin da mutane da suka zaɓe ni ke nuna damuwa a kai, ko hankalinsu yake kai. Na ga tunanin mutane da damuwar da suke nuna yadda ran ɗan adam ya koma kamar ba na ɗan dama ba.
“Yadda ake karya dokokin yaƙi da mutuntaka ta ƙasa da ƙasa, dole mu yi magana,” in ji Sanatan.
Ita ƙasa ba zaman kanta take yi ba zaman al’umma take in shi, kuma idan ta bauɗe sai muja hankalinta a matsayinmu na wakilan ƙasa.
Wakilin BBC ya tambayi sanatan kan cewa ba sa ganin matakin da suka ɗauka zai iya shafar dangantakar Najeriya da Isra’ila, musamman inda take cewa babu batun tsagaita wuta har sai an sako mutanenta da aka yi garkuwa da su?
Sai Kawu Sulamaila ya ce, “abin ba iya Najeriya ba ne, Afrika ta Kdu da Shugabanta sun tsaya sun bayyana matsayarsu a fili. MDD ta bayyana matsayarta a duniya a fili game da wannan yaki.
“Kasashe da dama sun fito sun bayyana matsayinsu kan Isra’ila na amfani da ƙarfin da ya wuce ƙima kan Falasɗinu, kan mata da yara da tsofaffi da wuraren idaba wanda bai kamata ba.
“Idan wani zai ɓata rai yana yin zalunci ai ina ganin don ba zai ji ɗaɗi b aki ka yi shiru, in ji Kawu Sumaila.
Kudurin dai ya samu goyon bayan ‘yan majalisa kusan 45, waɗanda suka sama hannu gabainin a gabatar da shi gaban Majalisa.
A cewar Kawu Sumaila Majalisar ta yi na’am da wannan kudri.

BBC
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp
Muna jinjina ta musamman ga Seneta Kawu Sumaila. ALLAH sassaka Ya kara masa girman kujera da mukami