Habubakar Fulata, Shugaban Kwamitin Majalisar Wakilai kan Ilimin Jami’o’i ya yi kira da a kara albashi ga malaman Firamare, Sakandare da Jami’o’i.
Alfijir Labarai ta rawaito Shugaban ya ce ya kamata malamain firamare su rika daukar Naira 250,000, Sakandire N500,000 da kuma Naira miliyan 1 ga malaman jami’o’i a duk wata.
Fulata yayi wannan magana ne a wajen wani taron bita na kwana daya na masu ruwa da tsaki na kasa kan bunkasa taswirorin tsarin ilimi na Najeriya (2023-2027), a Abuja a yau Alhamis.
Ya ce yana da kyau malaman Najeriya su kara kwarin gwiwa ta hanyar biyan su kudaden da suka dace domin koyar da yara.
Ya kuma jaddada wajibcin fassara dukkan litattafan darussa zuwa harsunan cikin gida domin kamo matakin tsarin na duniya.
A cewarsa, gwamnatocin da suka shude sun yi kokari a fannin ilimin kasar amma hakan bai haifar da sakamakon da ake so ba.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/K8z1chFesJeCf99QehWJPo
Wannan bawan Allah, Allah Ya maka albarka Ya jikan iyayenka Ya kuma kara maka; lfy nisan da girman mukami a Nig. har ms ka zams shugaban kasa