Mai Martaba Sarkin Kano Ya Taya Zababben Gwamnan Kano Murnar Lashe Zaɓe

Alfijr ta rawaito mai martaba sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya taya zabbben Gwamnan Jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf murna bisa nasarar da ya samu ta lashe zaben gwamnan jihar a zaben da aka gudanar ranar Asabar, 18 ga Maris.

Sakataren Yada Labarai na Masarautar Kano, Abubakar Balarabe Kofar Naisa, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ga manema labarai.

Ya ce Sarkin ya bayyana cewa al’ummar jihar sun karbi tsarin mulkin damokaradiyya da matukar muhimmacin idan akayi la’akari da yadda su ka fito domin jefa kuri’unsu kamar yadda tsarin mulki ya bada dama.

Sarkin ya kuma shawarci, tare da kira ga sabon gwamnan da ya hada kai da dukkanin rukunin al’umma wajen tafiyar da gwamnati, domin yin hakan zai taimaka wajen kyautata rayuwar al’umma da kuma kawo cigaban da ake bukata domin bunkasar tattalin arziki ga jihar Kano da kasa baki daya.

Sanawar ta kuma godewa malamai da Limamai da sauran Al’umma bisa addu’ar zaman lafiya da suka dunga yi kafin da kuma bayan gudanar da zaben.

San Kano yayi fatan dorewar zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar Kano har ma da sauran sassan kasar nan.

Ya kuma yi wa Abba addu’ar kammala mulkinsa lafiya tare da samun cigaban gwamnatinsa da habaka tattalin arzikin jihar Kano.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/G1wNveF9mGU7jec5mWhFvZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *