MAI FARUWA TA FARU! Wani Almajiri Ya Fille Kan Wani Yaro A Garin Kanwa Kano

IMG 20240411 WA0029

Daga Aminu Bala Madobi

…A garin kanwa ta karamar hukumar Madobi.

Bayan kammala tattara bayanan farko da jaridar Alfijir tayi ta tabbatar da cewa wannan Almajiri dan shekara 20 a duniya yanke-take ya yanke wuyan wani yaro dan kimanin shekara 10 a duniya.

Alfijir labarai ta rawaito Almajirin da yayi wannan katobara daga bisani ya jefa kan yaron da ya gille cikin shadda (Masai) tare da daddabawa yaron wuka, inda yake a cikin jini.

Hakanan matashin almajiri dai yana zuwa garin na kanwa ne dake karamar hukumar Madobi domin karatun alkur ani, inda tsawon watanni uku da suka gabata sukayi bulaguro da malamin sa kasancewar sun dan saba da jamaa ya sake dawo garin.

Rahotanni sun ce almajirin yazo garin ne domjn yin bikin sallah karama. Hakanan bai tsaya a iya fille kan yaron ba, daga nan ya farke cikin yaron tare da fito da kayan cikinsa, duk a garin na Kanwa karamar hukumar Madobi dake nan jihar Kano.

Rahotanni sun ce tuni fusatttun matasa na wannan yankin su kai rajamu tare da kashe wannan Almajiri da yayi aika-aikar har lahira.

Yanzu an tura jami’an tsaro zuwa yankin kuma sun dauke gawarwakin guda biyu zuwa caji ofis na garin Kwankwaso domin fadada bincike.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/CJ2q8cmhhOxFY6OEgwV5vk

Rahotanni sun ce tuni fusatttun matasa awannan yankin sukai rajamu tareda kashe wannan Almajiri dayayi aika-aikar har lahira.

Yanzu an tura jami’an tsaro zuwa yankin kuma sun dauke gawarwakin guda biyu zuwa caji ofis na garin Kwankwaso domin fadada bincike.

Aminu Bala Madobi 11 Aprilu 2024.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *