Ma’aikatan Shari’ar Najeriya Sun Tsunduma Yajin Aiki Saboda Karin Fetur

Alfijr ta rawaito Kungiyar Ma’aikatan Shari’a ta Najeriya ta yi shelar tsunduma yajin aiki a kasar sakamakon matakin gwamnati na janye tallafin man fetur, inda a yanzu farashin lita guda ya ninka har sau uku idan aka kwatanta da yadda farashin yake gabanin shugaba Bola Ahmed Tinubu ya karbi mulki.

Wannan na zuwa ne bayan ita ma Kungiyar Kwadago ta Kasar NLC ta ayyana tsunduma yajin aiki gama-gari nan da ranar Laraba mai zuwa muddin gwamnatin ta gaza daukar wani mataki.

A yayin gabatar da jawabinsa na shan rantsuwar kama-aiki a ranar Litinin da ta gabata, shugaba Tinubu ya sanar da janye tallafin man fetur din, abin da ya sa nan take nasu sayer da man suka kara farashi a sassan kasar.

Yanzu haka gida mai na kamfanin NNPC na kasa na sayar da lita guda akan Naira 488 zuwa Naira 570, sababin Naira 197 da ake sayarwa gabanin janye tallafin.

RFI Hausa

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook.   Alfijr Labarai
YouTube.     Best Seller Channel
Twitter.        @Musabestseller
Instagram.  @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/GdLiqZyHuSz5NhjdGoGRGZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *