Alfijr ta rawaito Ma’aikatar Sharia ta jihar Kano(Ministry of justice ta musanta rade-radin cewar Antoni janar zai yi amfani da ikon sa na doka domin sakin Alasan Ado Doguwa.

Babban mai gabatar da kara akan Shari’ar Barr. Abba Lamido Soron Dinki ne ya bayyana cewar, babu wannan maganar kuma basu dauki Shari’ar zargin kisan kai da akewa
Doguwa da wasa ba.

Ya kuma kara da cewar, babu wani shiri na sakin sa Ko kuma yiwa Shari’ar sa kafar Ungulu.
Freedom Radio

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇