Lafiya: An Sake Dakatar Da Wani Likita A Asibitin Kwararru Na Murtala A Kano

Shugaban hukumar kula da asibitocin jihar Kano, Dakta Mansur Mudi Nagoda, ya sake dakatar da wani likita a asibitin kwararru na Murtala Muhammad.

Alfijir Labarai ta rawaito ana zargin likitan ya bar aikin sa ne a daren ranar Litinin da ta gabata.

Dr Nagoda wanda ya kai ziyarar bazata da karfe 12 na dare har zuwa karfe 5 na Asuba, ya tarar da rashin likita a bakin aiki kuma bai iya samunsa ko a waya ba.

Shugaban kula da asibitocin ya koka da cewa bayan dakatarwar da aka yi wa wasu likitoci a ranar Litinin, yace wannan zata zamarwa  sauran likitoci da ma’aikatan jinya da ke wasu cibiyoyin lafiya izna wajen daukar ayyukansu da muhimmanci.

Idan dai za a iya tunawa hukumar ta dakatar da wasu shugabannin asibitoci uku a jihar Kano inda ma’aikatan lafiya suka kauracewa ayyukansu a daren ranar 30 ga watan Yuli da ya gabata.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook.   Alfijir Labarai
YouTube.     Best Seller Channel
Twitter.        @Musabestseller
Instagram.  @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai  👇

https://chat.whatsapp.com/BW0j8s7exuQ7ojpyCVMtfI

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *