Labari Mai Dadi! Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta kama wanda ya kashe Daliba Nabeeha

FB IMG 1706438684895

Rundunar ‘yan sandan Najeriya, a ranar 20 ga Janairu, 2024, ta kama wani Bello Mohammed, mai shekaru 28, dan jihar Zamfara, a Kaduna.

Alfijir labarai ta rawaito wanda ake zargin, yayin da ake yi masa tambayoyi, ya amsa cewa yana cikin kungiyar da ta yi garkuwa da dangin wani Barista Ariyo a Bwari, FCT, a ranar 2 ga Janairu, 2024, tare da kashe wasu da aka yi garkuwa da su, ciki har da Nabeeha, yar lauya, 13 ga Janairu, 2024, a sansanin masu garkuwa da mutane, a jihar Kaduna.

Wanda ake zargin, a cikin wani yanayi mai ban mamaki, ya bayar da #1,000,000 (Naira miliyan daya kacal) don jawo hankalin DPO, wanda ya ki amincewa da tayin, kuma ya gudanar da aikinsa da himma.

Radio Nigeria

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H3iC9eVfJI012LJzvCQn5V

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *