Labari Mai Dadi! Kotun Koli Ta Amince Da Bukatar Gwamnatin Tarayya Akan Kananun Hukumomi

FB IMG 1718289222877

A ranar Alhamis din da ta gabata ne dai kotun kolin kasar ta kebe hukunci a gaban wata kara da gwamnatin tarayya ta shigar a kan gwamnonin jihohin kasar nan 36 kan rashin da’a da ake yi a kananan hukumomin.

Alfijir labarai ta ruwaito kararrakin da Babban Lauyan Tarayya (AGF) da Ministan Shari’a, Lateef Fagbemi ya shigar, na neman cikakken ‘yancin cin gashin kai ga daukacin kananan hukumomin kasar.

A cikin karar, gwamnatin tarayya ta yi batu ingantacce na musamman ga kotun da ta bayar da umarni, tare da haramta wa gwamnonin jihohi rusa shugabannin kananan hukumomi, ba bisa ka’ida ba.

Gwamnonin jihohin kasar 36 sun kai kara ne ta hannun babban Lauyan su.

Har ila yau karar na neman a bada umarnin a ba su kudaden da ke hannun kananan hukumomi kai tsaye daga asusun tarayya kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar ya tanada wanda ya sabawa asusun hadin gwiwa da gwamnoni ke yi.

Gwamnatin tarayya ta kuma roki kotun koli da ta bada umarnin dakatar da gwamnoni ci gaba da kafa kwamitocin riko domin tafiyar da al’amuran kananan hukumomi wanda ya sabawa tsarin mulkin dimokuradiyya da tsarin mulki ya amince da shi.

Hakazalika ta nemi a ba da umarnin hana gwamnoni da wakilansu da masu fafutuka daga karbar ko kashewa ko kuma yin cuwa-cuwa da kudaden da aka fitar daga asusun tarayya domin amfanin kananan hukumomi idan ba a samar da tsarin kananan hukumomi na dimokuradiyya a jihohin ba.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *