Gwamnan jihar Rivers a kudancin Najeriya, Siminalayi Fubara, ya biya wa maniyyata aikin Hajjin bana daga jihar cikon naira miliyan daya da dubu dari tara na kuɗin kujerun.
Alfijir labarai ta rawaito farkon makon nan ne Hukumar Alhazan Najeriya ta bayyana ƙarin kudin, tana mai alaƙanta matakin da faɗuwar darajar naira.
Gwamnan dai ya dauki wannan mataki ne a kokarin cika alkawarin da ya yi wa jama’ar jihar a lokacin yaƙin neman zabe, cewa zai tafi da kowa a gwamnatin ba tare da nuna bambancin addini ko ƙabila ba.
Alhaji Yakubu Aliyu, daya ne daga cikin shugabannin ‘yan arewacin Najeriya mazauna jihar ta Rivers, kuma ya yi karin bayani a hirarsa da Abdussalam Ibrahim Ahmed.

BBC
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/CJ2q8cmhhOxFY6OEgwV5vk