Labaran Duniya Na Yammacin Lahadi 03/12/2023 – 19/05/1445AH

best seller i

Daga Baba Usman Gama

Shugaba Tinubu ya warewa Buhari, Osinbajo da Jonathan Naira Biliyan 13 a Kasafin Kudin 2024.

Dan takarar gwamnan jam’iyyar NNPP a jihar Taraba ya garzaya Kotun Koli.

An samu mummunan hatsarin mota a kan titin hanyar Ogbomosho zuwa Oyo wanda ya salwantar da rayukan mutum tara.

‘Yan Najeriya na korafin tawagar mutane dubu 1 da dari 4 da suka je taron COP28.

Najeriya za ta cigaba da tattaunawa don sako hambararren shugaban Nijar Bazoum.

An sanar da kotun koli a shari’ar Gwamanan jihar Kano cewa kuri’un NNPP 1,886 ne wadanda ba halatattu ba, amma 88.33% sun cika ka’idojin zabe.

SERAP ta nemi majalisa ta yi watsi da bukatar gina wa Shettima gidan N15bn.

A wani yunkuri na neman sauki, Alvin Ilenre, dan Najeriya mai digiri dan asalin jihar Edo, ya kona takardar digirinsa.

‘Yan sanda a jihar Kano sun tabbatar da kama mai ba Gwamnan jihar shawara ta musamman, Tasiu Al’amin-Roba da wani Abdulkadir Muhd kan zargin karkatar da kayan tallafin jihar.

Wasu jami’an ƴan sandan jihar Rivers sun shiga hannu bisa zargin sace wani matashi da neman kuɗin fansa.

Shugabannin ECOWAS za su yi taro a Abuja babban birnin Nijeriya a ranar 10 ga watan Disamba domin tattaunawa kan halin da yankin na Yammacin Afirka yake ciki.

Shugaban Guinea-Bissau Umaro Sissoco Embalo ya ce wadanda suka yi “yunkurin juyin mulki” a kasar a makon jiya za su dandana kudarsu.

Dakarun wanzar da zaman lafiya na kasashen gabashin Afrika sun fara ficewa daga Jamhuriyar Congo.

Mutum daya ya mutu wasu sun samu rauni a harin wukar da wani ya kai a Paris.

NPFL: Pillars ta samu nasara akan Gombe United da ci 5:2 a wasan yau.

EPL: Chelsea ta sami nasara akan Brighton da ci 3:2 a wasan yau.

EPL: Liverpool ta sami nasara akan Fulham da ci 4:3 a wasan yau.

EPL: Manchester City da Tottenham sun tashi 3:3 a wasan yau.

Bundesliga: Dartmound da Liverkusen sun tashi 1:1 a wasan yau.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *