Kwamishinan Ƴan Sanda Ya Cire wani DPO da yaransa Kan zaluntar wasu

FB IMG 1668778250057

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Legas, Idowu Owohunwa, ya bayar da umarnin korar jami’in ‘yan sandan Dibisional (DPO) na ofishin ‘yan sanda na Meiran da ke jihar Lagos bisa zargin karbar kudi.

Alfijir Labarai ta rawaito Tun da farko, wani Injiniya Ibrahim Saliu, wanda ya zanta da kamfanin dillancin labarai na PUNCH, ya yi ikirarin cewa wasu ‘yan sandan da ke aiki a ofishin ‘yan sanda na Meiran a jihar Legas sun karbo masa Naira 200,000 a ranar Asabar.

A cewar Saliu, jami’an tare da DPO sun yi barazanar daure shi da dan uwansa idan har suka kasa ba da takardar shaidar wayar da aka gani tare da dan uwan Saliu.

Ya ce, “DPO ya dauki wayoyin iPhone, ya cire takardar garanti, sannan ya bayyana cewa ni da dan uwana barayi ne kuma ’yan fashi da makami ne.

Abu na gaba da na ji shi ne DPO ya ba su umarni a tsare mu kuma za a tsare mu da laifin sata da fashi da makami. Mun yi mamaki.

Saliu ya bayyana cewa an nemi ya biya su Naira 500,000 domin samun ‘yancinsu. Sun amince da Naira 200,000, wanda aka biya a tsabar kudi bisa ga umarnin jami’an.

A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter da ke tabbatar da faruwar lamarin a ranar Laraba, jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, Benjamin Hundeyin, ya bayyana cewa, CP Legas ya bayar da umarnin tsige DPO na ofishin ‘yan sanda na Meiran cikin gaggawa.

Hundeyin ya rubuta, “CP Idowu Owohunwa ya ba da umarnin a tsige DPO Meiran nan take saboda rashin adalci da kuma rashin bin doka da oda.

“A halin da ake ciki, an gano dukkan jami’an da abin ya shafa kuma a halin yanzu suna hedikwatar rundunar inda aka fara bincike akansu.”

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/K8z1chFesJeCf99QehWJPo

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *