Rundunar ‘yan sandan Najeriya kungiya ce mai da’a sosai, kuma ba za ta taba amincewa da rashin da’a na jami’in da aka gani a bidiyon ba.
Alfijir Labarai ta rawaito kwamishinan ‘yan sandan jihar Imo, Muhammed Barde, ya bayar da umarnin kama wani dan sanda Sufeto da aka kama a wani faifan bidiyo yana mari wani direba akan hanya a jihar.
Lamarin da ya afku a Owerri, babban birnin jihar, ya janyo martani daga ‘yan Najeriya, inda suka bayyana hakan a matsayin rashin mutuntaka ga wanda abin ya shafa.
Yayin da yake bada Umarnin a kamo dan sandan da ya yi laifin, Barde ya ba da umarnin a kama jami’in nan take.
A wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na jihar, ASP Henry Okoye, ya fitar a ranar Laraba, CP ya yi Allah wadai da rashin da’a na jami’an ‘yan sanda.
Ya ba da umarnin a gano jami’in tare da kama shi nan take, yana mai cewa ba za a amince da abin da jami’in ya yi ba.
Sanarwar ta ce: “An jawo hankalin rundunar ‘yan sandan jihar Imo kan wani faifan bidiyo mai dauke da taken; “’Yan sandan Najeriya ba za su taba zama Abokinka ba musamman na garin Owerri”, inda aka ga wani Sifeton ‘yan sandan da ake zargin yana aiki a Jihar Imo da karfi ya cire hular wani matashi tare da yi masa mari a fuska.
“Kwamishanan ‘yan sandan jihar Imo, CP Muhammed Ahmed Barde, ya yi Allah-wadai da wannan aika-aika gaba daya domin ya sabawa ka’idojin kwararru da ka’idojin rundunar.
Rundunar ‘yan sandan Najeriya kungiya ce mai da’a sosai, kuma ba za ta taba amincewa da rashin da’a na jami’in da aka gani a bidiyon ba.
“Saboda haka, CP ya umurci tawagar sa ta sa ido ta gudanar da bincike tare da gano jami’in don daukar matakin ladabtarwa.
“Bugu da ƙari, ana ƙarfafa wanda abin ya shafa ya kira PPRO Imo akan 08148024755 ko kuma ya zo sashin hulda da jama’a na ‘yan sanda Owerri ya gabatar da kokensa.”
A cikin wani bayani da aka samu bayan ‘yan sa’o’i kadan, kakakin ‘yan sandan ya sanar da cewa an gano sifeton ‘yan sandan da ya yi laifin tare da kama shi.
Okoye ya ce a halin yanzu dan sandan yana fuskantar shari’a a cikin wani kwamati da aka samar, kuma za a dauki matakin ladabtarwa a kansa.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijir Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/Jmw5CBsPV6H3DbSgnlFUHM