Kurunkus: Kotu ta yanke hukuncin zaben gwamnan jihar Bauchi

Kotun sauraron korafe-korafen zaɓen gwamnan jihar Bauchi, a yau ta tabbatar da nasarar da gwamna Bala Mohammed na jam’iyar PDP, ya samu a zaɓen ranar 18 ga watan Satumba, da ala gudanar a jihar.

Alfijir Labarai ta rawaito Kotun sauraron korafin zaɓen ta kori ƙarar da jam’iyar APC da ɗan takararta Air Marshal Sadique Abubakar mai ritaya su ka shigar gaban ta su na kalubalantar nasarar gwamna Bala.

Kotun ta ce babu wani dalili da zai jawo a soke zaɓen, domin an gudanar da shi akan doron shari’a.

Hukuncin na zartar da shi ne bisa kulawar alkalai guda uku ƙarƙashin jagorancin mai shari’a P.T. Ƙwahar.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/FNim39ly65N2CzcTt8FgWb

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *