
Alfijr ta rawaito Kungiyar kwallon kafa ta Paris Saint-Germain ta dakatar da Lionel Messi na tsawon makwanni biyu ba tare da wani bata lokaci ba.
Hakan ya faru ne biyo bayan tafiyarsa ba tare da izini ba zuwa Saudi Arabiya, bayan rashin nasara da suka yi da Lorient da ci 3-1 a karshen makon da ya gabata.
Romao ya wallafa hakan ne a shafinsa na Tuwita cewa: “Paris Saint-Germain ta yanke shawarar dakatar da Lionel Messi nan da nan na tsawon makonni biyu.
Dakatarwar za ta gudana ne a yanzu bayan tafiyar Messi zuwa Saudiyya ba tare da bada izini daga kulob din ba kamar yadda @RMCsport ta ruwaito. ”
Kocin PSG Christophe Galtier ya yi wa ‘yan wasansa alkawarin cewa za su samu hutun kwanaki biyu wato Litinin da Talata idan suka doke Lorient a ranar Lahadi.
Sai dai Galtier ya bayyana cewa rashin nasara zai sa ‘yan wasan za su je atisaye ranar Litinin.
Messi ya bukaci tafiya zuwa gabar tekun Larabawa don girmama yarjejeniyar daukar nauyinsa a matsayin jakadan Saudiyya.
Galtier da darektan wasanni Luis Campos sun ba shi izinin tafiya ne kawai idan PSG ta yi nasara ko kuma ta yi canjaras, amma ba rashin nasara ba.
Sai dai bayan da aka doke Lorient da ci 3-1, Messi ya garzaya Saudiyya ba tare da ya sake neman izini ba, wanda hakan ke nufin ba zai iya halartar atisaye a ranar Litinin ba.

Hukumar kwallon kafa ta La Liga ta ba da wasu manyan sharudda uku da za a cika kafin Lionel Messi ya koma tsohuwar kungiyarsa. Kamar yadda Daily Post ta ruwaito.
Shugaban La Liga, Javier Tebas ya bayyana hakan ne yayin da yake magana kan yiwuwar dawowar Messi zuwa gasar ta Sidaniya kamar yadda makomar dan wasan mai shekaru 35 ta kasance abin magana a kwana kwanan nan.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu aFacebook. Alfijr Labarai YouTube. Best Seller ChannelTwitter. @MusabestsellerInstagram. @musa_bestsellerKo a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇https://chat.whatsapp.com/G1wNveF9mGU7jec5mWhFvZ