Kungiyar mawakan Hausa sun nemi afuwar Buhari kan kalaman Rarara

Screenshot 20231031 170252 com.facebook.katana edit 106985140207631

Kungiyar mawakan hausa da ake kira (One Voice Association) sun barranta kansu da kalaman mawaki Rarara na sukar tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Alfijir Labarai ta rawaito cikin wani bidiyo da ya karade kafafen yada labarai sun nuna yadda Rarara ya kalubalanci gwamnatin Buhari, inda ya bayyana ta a matsayin mara nasara data haddasa wahala ga ‘yan kasa.

Saidai kuma kungiyar (One Voice Association) ta bayyana rashin amincewar ta da kalaman Rarara, mambobin kungiyar sunce Rarara yayi kalaman ne a karankansa.

Shugaban kungiyar Ali Jita, yace a matsayin su na mawaka suna girmama manya da sauran mutane da suka shugabanci kasar nan batare da la’akari da kabila ba.

Ali Jita, yace kalaman Rarara sun saba da tarbiya da dabi’un mawaka.

Yace kamar kowane mutum shugaba Buhari yana da matsalolin sa amma duk da yayi iya nasa kokarin a kasar nan.

Mataimakin kungiyar Ado Isah Gwanja ya bayyana shirin su na ziyartar tsohon shugaban kasa Buhari a Daura domin neman afuwar sa kan kalaman da Rarara yayi masa.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp

One Reply to “Kungiyar mawakan Hausa sun nemi afuwar Buhari kan kalaman Rarara”

  1. Sai su yi ta yi, tunda wahala ba ta ice su ba! Za su masifa da wahala har gidanta bayan da Allah Ya raba mu da ita, duk da cewa ma har yanzu muna ji a jikinmu kamar muna cikin toka mai dumi!!
    Buhari da Rara dukkansu macutan ‘yan Nijeriya ne!!! Sai dai Allah kadai zai saka mana.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *