An Ja Kunnen Zaɓaɓɓen Shugaban Ƙasa Kan Shugabancin Majalisar Dattawa

Alfijr ta rawaito Sanata na jam’iyyar APC ya jajirce kan cewar Kundin tsarin mulkin ne zai yanke hukunci a kan shugaban majalisar dattawa, ba kai ba –

Sanatan Zamfara ta Yamma, Abdul’Aziz Abubakar Yari, ya ki amincewa da lallashin zababben shugaban kasa, Bola. Tinubu, ya janye wa Sanata Godswill Akpabio a takarar shugabancin majalisar dattawa, yana mai cewa zai ci gaba da tsayawa takara.

Yari, wanda tsohon gwamnan jihar Zamfara ne, ya ce za a yi takarar shugabancin majalisar dattawa ne bisa tanadin tsarin mulki ba umarnin kowa ba.

Ya ce, “Abin da zai faru a wannan rana, zai faru ne bisa ga umarnin tsarin mulki ba na kowa ba.”

Tsohon dan majalisar wakilai ya bayyana takarar a matsayin sanatoci, wanda tsarin mulkin 1999 ya goyi bayan su zabi shugabanninsu a cikin su ba bisa umarnin kowa ba.

A ranar Juma’ar da ta gabata ne jam’iyyar APC mai mulki karkashin jagorancin Tinubu ta amince da Akpabio a matsayin wanda ya fi son tsayawa takarar shugaban majalisar dattawa a majalisar dattawa ta 10 mai zuwa.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/G1wNveF9mGU7jec5mWhFvZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *