Kotun Zaɓe ta tabbatar da zaben ɗan majalisar dokokin Kano na NNPP

Kotun sauraron kararrakin zabe ta Majalisar Dokokin Jiha ta kasa, a yau Litinin, ta tabbatar da zaben Mudassir Zawachiki na jam’iyyar New NNPP a matsayin dan majalisa mai wakiltar mazabar Kumbotso a majalisar dokokin jihar Kano.

Alfijir Labarai ta rawaito yayin hukuncin da suka yanke, kwamitin alkalai uku karkashin jagorancin Mai shari’a L. B. Owolabi, sun yi watsi da bukatar Sagir Abdulkadir-Panshekara na jam’iyyar APC, inda suke kalubalantar nasarar Zawachiki a zaɓen da aka gudanar a ranar 18 ga Maris, 2023.

Alkalan sun ce mai shigar da kara ya gaza tabbatar da zargin aringizon kuri’u, tashin hankali da amfani da takardar sheda ta jabu ba tare da wata shakka ba.

“Mai shigar da karar ya kasa tabbatar da rashin bin dokar zaben 2022 da sauran kura-kurai.

Da yake mayar da martani, Zawachiki ya shaida wa manema labarai jim kadan bayan nasararsa, “Na gode wa Allah Madaukakin Sarki gaskiya ta yi nasara. Zan ci gaba da yin iya ƙoƙarina don tabbatar da amincewar da aka yi min.”

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai  👇

https://chat.whatsapp.com/FNim39ly65N2CzcTt8FgWb

One Reply to “Kotun Zaɓe ta tabbatar da zaben ɗan majalisar dokokin Kano na NNPP”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *