Bayan fara kwato bashin noma yanzu bankin Najeriya ya fara zaftare rancen Covid-19

Bayanai daga Najeriya na cewa babban bankin kasar CBN ya fara aiwatar da matakin karbo rancen da ya baiwa wasu ‘yan kasar domin saukaka musu radadin kuncin tattalin arzikin da barkewar annobar Korona ta haddasa a sassan duniya

Alfijir Labarai ta rawaito babban bankin Najeriyar dai ya bayar da tallafin rancen korona ne a tun shekarar 2020, shi kuma na manoma shekarar 2015, domin inganta ayyukan noma.

Bayanai sun ce tuni bankin na CBN ya fara cire kudaden da yake bin wasu da ya bai wa rancen daga asusunsu, sai dai wasu na korafi akan tsarin da ake bi wajen karbar kudaden, inda a maimakon a rika janye musu kudaden a hankali, sai a rika zaftare jimillar adadin kudaden tallafin da suka amfana da shi a lokaci guda, abinda suka ce yana matukar jefa su a cikin kuncin gurguncewar gudanar da harkokinsu na yau da kullum.

Wani batu kuma da a yanzu yake daukar hankali shi ne alwashin da gwamnatin Najeriya ta yi na kammala karbo tallafin rancen kudaden da ta bai wa dubun dubatar manoman kasar a karkashin shirin ‘Anchor Borrower’ da aka fara a shekarar 2015.

A wannan Litinin ne dai wa’adin da shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya kayyade na tabbatar da cewa an karbo bashin noman daga wadanda suka amfana ya cika.

Babban bankin Najeriya ya ce zuwa shekarar 2022, manoma akalla miliyan 4 da dubu 800 ne suka samu tallafin shirin bunkasa noman na ‘Anchor Borrower’, sai dai akasarin wadanda suka amfana da tallafin rancen basu mayar da kudaden ba, duk kuwa da cewar farashin albarkatun gonar da suka noma ya karu sosai.

Wani rahoton asusun ba da lamuni na duniya IMF ya nuna cewar, kashi 76 cikin 100 na adadin kudaden rancen da bankin CBN ya bai wa monama a Najeriyar ne ba a maida ba.

Wannan ce ta sanya sabon shugaban Najeriya shan alwashin kawo karshen matsalar.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/FNim39ly65N2CzcTt8FgWb

One Reply to “Bayan fara kwato bashin noma yanzu bankin Najeriya ya fara zaftare rancen Covid-19”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *