Kotun Ta Daure Wani Lauyan Bogi Ɗan Jarida Bogi Watannk 15 A Kano

An gurfanar da wani lauyan bogi mai suna Zaharaddin Sani Maidoki a gaban kotun shari’ar Musulunci bisa zargin yaudara da cin amana.

Alfijir Labarai ta rawaito Kotun da ke zamanta a karamar hukumar Kiru da ke jihar Kano karkashin mai shari’a Abdulmuminu Nuhi ta daure wanda ake zargin a gidan gyaran hali da tarbiyya watanni 15 da tarar N20,000.

Wanda ake zargin wanda dan asalin jihar Kaduna ne ya bayyana kansa a matsayin lauya da niyyar kare wasu mutane a gaban kotu.

Zaharaddin ya amsa dukkan tuhume-tuhumen da ake kararsa akai wanda ya hada da bayyana kansa a matsayin dan jarida daga jihar Kaduna.


Yayin yanke hukuncin, Alkalin kotun ya daure matashin tare da yin amfani da dokokin shari’a ta jihar Kano karkashin sashe na 337.

Kotun har ila yau, ta tura sako zuwa Kungiyar Lauyoyi ta jihar Kaduna don tabbatar da ikirarin shi lauya ne, inda kungiyar ta ce ba ta san da zamanshi a kungiyar ba.

Alkalin kotun ya shaida masa cewa yana da kwanaki 30 idan bai gamsu da hukuncin kotun ba zai iya daukaka kara.

Kotun ta kuma kwace dukkan wasu takardu da ke tare da shi da kuma shaidar katin aiki da yake ikirarin shi lauya ne kuma dan jarida.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook.   Alfijir Labarai
YouTube.     Best Seller Channel
Twitter.        @Musabestseller
Instagram.  @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai  👇

https://chat.whatsapp.com/GdLiqZyHuSz5NhjdGoGRGZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *