Kotun Soji Ta Kama Wani General Da Laifin Satar Fiye Da Biliyan Daya A Najeriya

FB IMG 1696575644420 edit 8390611110175

Kotun Sojin Najeriya ta musamman da ke zamanta a Abuja ta ce ta samu Maj-Gen Umaru Muhammed da laifin satar $1.476m.

Alfijir Labarai ta rawaito Shugaban kotun, Maj.-Gen. James Myam, ya ce a ranar Larabar da ta gabata, a yayin da ake shari’ar, wanda ake tuhumar, ya ki amsa laifinsa, inda ya gabatar da shaidu biyu.

Ya ce kotun ta samu wanda ake kara da laifin satar dalar Amurka miliyan 1.04 tsakanin 7 ga Mayu, 2019, zuwa 24 ga watan Yuni, 2021, a lokacin da yake aiki a matsayin GMD na NAPL.

Shugaban kotun ya kara da cewa, an samu wadanda ake tuhumar da laifin umurtar wani Manjo Usman da ya ajiye kudaden a asusun banki.

Mista Myam, ya ce ba a sami Mista Muhammed da laifi ba a shari’a ta 7, wanda ke da iyaka da hada baki da laifuka na jabun takarda tare da wani Yusuf Abdulahi.

Sai dai an same shi da laifin yin karya dangane da tuhume-tuhume 8 da 9 na satar dala 430,800, in ji shugaban kotun.

Kotun ta kuma samu Janar din da laifin hada baki wajen hada takardu, da kuma sayar da kadarorin kamfanin a lokacin da ya daina aiki a NAPL kan Naira miliyan 200.

Ta kuma same shi da laifin rashin gaskiya da karbar Naira miliyan 74 daga asusun kamfanin a ranar 22 ga Agusta, 2019.

Dalilin Da Yasa Muka Amince Da Balarabe Duk Da Cewar Ya Fadi A Lokacin Tantancewa-Majalisa

A kan tuhume-tuhume 14, 15, 16, da 18, wadanda ke da alaka da karkatar da kudade da sauran laifuka, kotun ta ce wadanda ake tuhumar ba za su iya bayarda lissafin Naira biliyan 2.5 na kamfanin ba.

A shari’a 17, inda ake tuhumar Janar din da fitar da Naira miliyan 750 daga asusun kamfanin, kotun ta ce masu gabatar da kara sun gaza tabbatar da zargin nasu ba tare da wata shakka ba.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai  👇

https://chat.whatsapp.com/FNim39ly65N2CzcTt8FgWb

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *