Kotun Koli Za Ta Saka Ranar Yanke Hukunci Kan Zaben Gwamnan Filato

FB IMG 1704888841491

Kotun koli ta sanya ranar Juma’a domin yanke hukunci kan rikicin zaben gwamnan Jihar Filato tsakanin PDP da APC

Alfijir labarai ta rawaito kotun Koli ta sanya ranar Juma’a domin yanke hukunci kan rikicin zaben gwamnan Jihar Filato.

Sakataren yada labarai APC na jihar, Sylvanus Namang, ya tabbatar wa Aminiya hakan a ranar Alhamis, inda ya yi kira ga ’yan Jam’iyyar su kwantar da hankalinsu, su bi doka da oda.

A baya dai kotun daukaka kara ta soke hukuncin kotun kararrakin zabe da ta tabbatar da zaben gwamna Caleb Mutfwang na Jam’iyyar PDP, tare da bayyana dan takarar APC a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar da aka gudanar a ranar 18 ga watan Maris.

Kotun daukaka kara ta bayyana cewa, takarar Gwamna Mutfwang harmtacciya ce, saboda jam’iyyarsa ta saba umarnin kotuna kan sake gudanar zabukan shugabannin mazabu zuwa matakin jiha.

Sakamakon rashin gwamsuwa da hukuncin kotun daukaka kara ne PDP ta garzaya kotun koli.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/IUuk7jeH4yvAkwOmbOCSfl

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *